iPhoneAddict Apps
  • Actualités
  • Accueil Apps
  • iPhone
  • iPad
  • Universelles
  • Mac
  • Apple TV
KG KultureGeek
App
iPhone / iPad Télécharger iAddict v5 Mac Télécharger iAddict Mac
  • Actualités
  • Accueil Apps
  • iPhone
  • iPad
  • Universelles
  • Mac
  • Apple TV
  • Archives keynotes
  • Firmwares & iTunes
  • Contactez-nous
  • Comparateur de prix
  • KultureGeek
Accueil » Liste des Apps » Apps Universelles » Education » Alƙurani Mai Girma Hausa Quran
1.1 iOS €1,99€ Abdulkarim Nasir 0 0 THE COMPLETE HOLY QURAN HAUSA TRANSLATION | Quran Hausa translation | Quran Hausa PDF | Quran in Arabic and Hausa Al-ƙur'ani mai Girma Fassarar Marigayi Malam Abubakar Mahmoud Gumi wanda a shekarar 1987 ya samu lambar yabo ta Sarki Faisal daga...
Alƙurani Mai Girma Hausa Quran

Alƙurani Mai Girma Hausa Quran

iOS Universel / Education

1,99€
Acheter sur l'App Store
Facebook X E-mail

THE COMPLETE HOLY QURAN HAUSA TRANSLATION | Quran Hausa translation | Quran Hausa PDF | Quran in Arabic and Hausa

Al-ƙur'ani mai Girma Fassarar Marigayi Malam Abubakar Mahmoud Gumi wanda a shekarar 1987 ya samu lambar yabo ta Sarki Faisal daga ƙasar Saudiyya saboda fassarar Al-Qur'ani mai girma zuwa harshen Hausa. Wannan Manhajja na aiki ba tare da data ba.

A wannan manhajja ta Alƙur'ani mai Girma zaku samu abubuwa kamar haka:
1. Cikakken karatun Al-ƙur'ani mai Girma muryar Sheikh Mahmoud Khalil Al-Hussary daga baƙara zuwa Nasi
2. Alƙurani bugon hannu na Malam Mahiru Sharif Bala Kano wanda shi wannan qur'ani akan yi masa laƙabi da Al-Qur'an Warsu irin wanda alarammomi ke amfani dashi a makarantunmu na Allo wato tsangaya
3. Al-ƙur'ani Mai Girma izufi sittin fassara da kuma wallafar marigayi malam Abubakar Mahmoud Gumi daga Harshen Larabci zuwa Harshen Hausa. Malam Abubakar Gumi ya sami lambar yabo da karramawa daga kasar Saudiyya sakamakon wannan fassara ta Al-ƙur'ani Mai Girma da yayi daga Larabci zuwa Hausa
4. Sashen fassarar Al-ƙurani Na Gumi na da tsari biyu jerin surori da kuma jerin juzu'i-juzu'i
5. Akwai kuma Al-ƙur'ani bugon madinah wasu kance dashi Al-ƙur'ani bugon misra da riwayar Hafs An Asim
6. Zaku iya canja launin rubutun Al-ƙur'ani bugon madinah zuwa fari, baqi, ja, kore ko shudi
7. Addu'o'in Alqunut daban-daban
8. Sunayen Allah dari ba daya audio

A daure a sauke Wannen manhajja domin samun amfanuwa da littafin Al-ƙur'ani Mai Tsarki duk da cewa tana da nauyi. Alƙurani Mai Girma wato Quran Hausa

Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an), ko kuma Alƙur'ani mai girma kamar yanda aka sani, shine littafin da Allah ya Saukar a harshen Annabin Rahama, wato Larabci, kuma shine littafin da Allah ya rufe saukar da duk wani Littafi Mai tsarki a bayansa.

Tarihin shigowar Musulunci a Kasar Hausa:
A game da kasar Hausa, tarihi ya nuna mana ba a shigo mana da musulunci ta hanyar karfi ba. A’a musulunci ya shigo mana ne ta hanyoyin fataucin kasuwanci da kuma matafiya na sa-kai don neman tarihin kasa da da’awa ta wa’azi da kuma hanyar kaurace-kaurace na kabilu da al’ummu daga wuri zuwa wuri kamar yadda ya gabata.

‘Yan kasuwa su ne suka fara shigowa da musulunci kasar nan (Najeriya), amma ta hanyar daidaikun mutane ne. Wasu ma suna ganin tun a farkon ƙarni na Hijirar Manzon Allah (S.A.W) musulunci ya fara saduwa da ƙasar Hausa ta gefen Katsina zuwa Kano, inda matafiya na kasuwanci suke bi daga wasu ƙasashe na Larabawa. Su ne kuma suka shigo mana da musulunci ta wannan hanyar zuwa arewacin Nijeriya.

Sannan hanya ta biyu ita ce ta wurin matafiya don rubuta tarihin ƙasa kamar su Ibn Khaldun da masu wa’azi kamar su Al-Maghili. Ta wannan fuskar sun fi mai da hankalinsu ta saduwa da sarakuna da mahukunta da malamai. A wannan hanyar ta biyu sun zo ne daga baya, kuma sun samu ƙasar Hausa cike take da mabiya addinin musulunci musamman ma talakawa. Watau dai a takaice talakawa sun fara karbar musulunci a kasar Hausa kafin sarakunansu su karbe shi. Misali, sarkin Katsina Korau (1320-1353) shi ne ya fara karbar addinin musulunci, sai sarkin Kano Yaji (1349-1385) wanda Wangarawa suka zo a lokacinsa, suka shigar da shi addinin musulunci. Sai sarkin Zazzau wanda ya musulunta na farko cikin sarakunanta shi ne Muhammadu Rabo. A masarautar Zamfara kuwa musulunci ya fara shigowa ne shekara ta 1640 A.D. Amma an ce ƙasar Zamfara ta karbi musulunci kafin 1640 A.D shi ne ingatacce. Haka dai sarakunan suka riƙa musulunta suna ƙarfafa Hakimai da Dagatai nasu a cikin musulunci da masu unguwanninsu har zuwa ga talakawa.
Misali, a zamfara akwai wasu malamai wadanda ake kira malamai na ‘Yan Doto. Su wadannan malamai suna ƙasar Zamfara tun shekaru aru-aru kafin bayyanar Shehu Usman dan Fodiyo. Wadannan malamai su ne ake kyautata zaton cewa su suka rubuta wasu shahararrun littattafai ‘yan ƙanana cikin ilimin Fiƙihu da Tauhidi da sauransu. Kamar littafin ƙawa’idi da Rashada da Ma’anar La’ilaha illallahu Muhammadur- Rasulullahi da makamantansu.

En voir plus...

Quoi de neuf dans la dernière version ?

1. Mun ƙara Tarjamar AlKur'ani daga Larabci zuwa Hausa kowacce aya an rubutata da Larabci, an rubutata da Hausar boko wato transliteration kana an rubuta fassararta da Turanci kuma an fassarata da Hausa.
2. Ku latsa aya domin samun options na aikewa da ita zuma ga yanzu.
3. Zaku iya rubuta lambar aya domin kaiwa gareta cikin sauƙi

  • Screenshot #1 pour Alƙurani Mai Girma Hausa Quran
  • Screenshot #2 pour Alƙurani Mai Girma Hausa Quran
  • Screenshot #3 pour Alƙurani Mai Girma Hausa Quran
  • Screenshot #4 pour Alƙurani Mai Girma Hausa Quran
  • Screenshot #5 pour Alƙurani Mai Girma Hausa Quran
  • Screenshot #6 pour Alƙurani Mai Girma Hausa Quran

D'autres applications du développeur

Siffatus Salatin Nabiyyi JafarSiffatus Salatin Nabiyyi JafariOS UniverselRediyon HausawaRediyon HausawaiOS UniverselUltimate Ruqyah Shariah MP3Ultimate Ruqyah Shariah MP3iOS UniverselEveryday Dua and Azkar OfflineEveryday Dua and Azkar OfflineiOS UniverselDua e Qunoot Offline MP3 &TextDua e Qunoot Offline MP3 &TextiOS UniverselKabiru GombeKabiru GombeiOS UniverselVoir toutes les apps

Note

(0 note)

Détails sur l'application

Version
1.1
Taille
688.6 Mo
Version minimum d'iOS
13.0
Dernière mise à jour
13/02/2025
Publié par
Abdulkarim Nasir

Newsletter App Store

Recevez chaque jour les meilleures promos

Actualité Apple

Image iOS 27 bêta 5 : la liste des nouveautés
iOS 27 bêta 5 : la liste des nouveautés
Image iOS 27 affiche désormais 5G+ pour la 5G SA avec la bêta 5
iOS 27 affiche désormais 5G+ pour la 5G SA avec la bêta 5
Image iPhone 18 Pro Max : la batterie avec une plus grosse capacité se confirme
iPhone 18 Pro Max : la batterie avec une plus grosse capacité se confirme
Image Release candidate pour iOS 26.6.1, iOS 18.7.10 et macOS 26.6.2
Release candidate pour iOS 26.6.1, iOS 18.7.10 et macOS 26.6.2
iPhoneAddict Apps

Le catalogue iPhoneAddict pour suivre les nouveautés, mises à jour et baisses de prix de l’App Store.

Apps

Toutes les apps iOS iPhone iPad Universelles Mac Apple TV

iPhoneAddict

Actualité Apple Archives keynotes Contact À propos KultureGeek

Suivez-nous

©2009-2026 i2CMedia. Tous droits réservés.