• KultureGeek
  • Comparateur de prix
       
iPhoneAddict
 iAddictv5Notre Application iPhone/iPad
  • Accueil Apps
  • Actualité Apple
  • Keynote Apple
  • Firmwares & iTunes
  • Contactez-nous
Accueil » Liste des Apps » Apps Universelles » Musique » Raddul Azhan Tafsirin Gumi MP3
1.0 iOS €2,99€ Abdulkarim Nasir 0 0 Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu 'yanuwa Musulmi, RADDUL AZHAN ILA MA'ANIL QUR'AN AUDIO / MP3 / OFFLINE / HAUSA LANGUAGE RADDUL AZHAN ILA MA'ANIL QUR'AN PDF IN HAUSA LANGUAGE Duba da kusantowar watan Ramadana na wannan shekara ta 2025...
Raddul Azhan Tafsirin Gumi MP3

Raddul Azhan Tafsirin Gumi MP3

iOS Universel / Musique

2,99€
Acheter sur l'App Store

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu 'yanuwa Musulmi,

RADDUL AZHAN ILA MA'ANIL QUR'AN AUDIO / MP3 / OFFLINE / HAUSA LANGUAGE
RADDUL AZHAN ILA MA'ANIL QUR'AN PDF IN HAUSA LANGUAGE

Duba da kusantowar watan Ramadana na wannan shekara ta 2025 (Allahumma ahillahu alayna bil-amni wal-iman was-salaamati wal-islam wa tawfeeq lima tuhibbu wa tardaa rabbuna wa rabbuka Allah), da kuma duba da yadda iyaye da kakanni ma'abota son jin tafsirin alkur'ani mai Girma na babban malamin nan malam Abubakar Mahmud Gumi muka ga ya kamata muyi kokari mu saukaka musu hakan ta hanyar samar da wannan manhaja ta Raddul Azhan ila Ma'anil Qur'an (MAYAR DA HANKULA ZUWA GA MA'ANONIN ALKUR'ANI) irinta ta farko a wannan dandali na Apple App Store. Tafsirin Raddul Azhan ila Ma'anil Qur'an shine tafsirin da Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi ya wallafa don fassara Al-Kur'ani Mai Girma. Yayi rubutun littafin ne cikin harshen Larabci wanda daga baya malamin ya fassara cikin sautin murya zuwa harshen Hausa.

Wannan manhaja ta kunshi muhimman abubuwa kamar haka:
1. Raddul Azhan ila Ma'anil Qur'an tafsirin malam Habubakar Gumi Audio / MP3 daga bakara zuwa Nasi *
2. Littafin Raddul Azhan ila Ma'anil Qur'an littafin larabci a sigar Raddul Azhan ila Ma'anil Qur'an PDF domin ma'abota karanta larabci suji dadin bin Tafsirin a lokacin da ake jawa malam baki yana fassara littafin.
3. Fassarar Alkur'ani mai Girma daga Larabci zuwa Hausa wato Tarjuma fassarar ayoyin kai tsaye zuwa harshen Hausa wanda shima malam Abubakar Gumi ne ya fassara.
4. Tarihin Malam Abubakar Gumi

Fasalin aikin Manhajjar:
1. Wannan app na aiki kacokam ba tare da intanet ba
2. A sashen fassarar ayoyin alkur'ani zaku iya danna aya domin samun damar sharing din fassararta ga yanuwa musulmi ta kafafenku na sadarwa
3. Idan kuka karanta fassarar ayoyin wata surah kana daga baya kuka rufe da sake bude wannan sura, to kuna iya ci gaba da karatun daga ayar da da kuka tsaya a kanta. Ku danna alamar dake sama-maso-dama kusa da search domin wannan zabin.
4. Akwai surori dake da ayoyi masu yawa kamar suratul Bakara mai ayoyi 286, domin zuwa fassarar wata aya kai tsaye, ku danna alamar nema kana ku rubuta lambar ayar da kuke son zuwa gareta sai ku danna kalmar "Muje" wato dai muje zuwa wannan ayar. App din zai kaiku kan ayar nan take.
5. Haka zalika a bangaren Raddul Azhan ila Ma'anil Qur'an pdf shima kuna iya rubuta lambar shafi domin tsallakawa zuwa gareshi ko kuma komawa farkon Tafsirin wata sura da kuka bude da dai sauransu.
6. Zaku iya saita timer domin jin Tafsirin na dan wani lokaci misali kafin kuyi bacci inda karatun zai rufe kansa da zarar lokacin ya cika. Misali kun kwanta bacci karfe tara sai kuka saita timer zuwa awa guda, to karatun zai rufe kansa da kansa da zarar karfe goma tayi.
7. Domin samun Muqaddimar littafin ku tsallaka zuwa shafi mai lamba ta 833.

* Muna kan Tarawa da daidaita wannan tafsiri har yanzu, fatanmu shine mubi tafsirin daya bayan daya domin rubuta lambobin dake kunshe a kowanne sauti kana ba tare da tsallake ba domin samar muku da cikakken Tafsirin na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi kamar yadda muka samar muku da Tafsirin Sheikh Jafar Mahmud Adam.

Muhimmiyar sanarwa:
1. Idan kuka sayi wannan app yanzu, baku bukatar sake karin biyan ko sisi bayan mun kammala update na app din da dora sabon version da kuma qara kudin shi app din. Ba za'a cajeku komai ba. Dukkan update zai zo muku kyauta ne
2. Idan kuka sayi wannan app, to ko kun canja wayarku ko kun goge app din da zarar kuna son sake sake saukeshi kuyi login da email din da kuka saya dashi a farko domin sake saukewa ba tare da sake biyan komai ba. Kuna iya saukewa a wayoyinku daban daban da email din da kukayi sayayyar farko dashi. Farashi daya rak za'a cajeku.
3. Farashin wannan app bai kai farashin huluna/takalmanku ba. Da fatan za'a daure a riqa sayen apps na musulunci marasa talla ciki.

Idan kunji dadin wannan manhaja, don Allah ku aiketa zuwa ga yanuwa domin su amfana da ita.
Domin tuntuba: kareemtkb@gmail.com
Ma'assalam.

En voir plus...

D'autres applications du développeur

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar
/ iOS Universel
Rediyon Hausawa
Rediyon Hausawa
/ iOS Universel
Ultimate Ruqyah Shariah MP3
Ultimate Ruqyah Shariah MP3
/ iOS Universel
Everyday Dua and Azkar Offline
Everyday Dua and Azkar Offline
/ iOS Universel
Dua e Qunoot Offline MP3 &Text
Dua e Qunoot Offline MP3 &Text
/ iOS Universel
Kabiru Gombe
Kabiru Gombe
/ iOS Universel
Voir toutes les apps

Note

(0 note)

Détails sur l'application

Version
1.0
Taille
644.7 Mo
Version minimum d'iOS
13.0
Dernière mise à jour
30/01/2025
Publié par
Abdulkarim Nasir

Newsletter App Store

Recevez chaque jour les meilleures promos

Actualité Apple

Image L’iPhone du 20ème anniversaire n’aurait plus de bordures autour de l’écran
L’iPhone du 20ème anniversaire n’aurait plus de bordures autour de l’écran
Image [#Promo] L’iPad 10 est proposé à seulement 299 euros sur Amazon !
[#Promo] L’iPad 10 est proposé à seulement 299 euros sur Amazon !
Image PayPal déploie en Europe, et sur iOS, son système de paiement tap-to-pay
PayPal déploie en Europe, et sur iOS, son système de paiement tap-to-pay
Image iPhone 18 Pro : nouvelle « confirmation » pour le capteur Face ID sous l’écran
iPhone 18 Pro : nouvelle « confirmation » pour le capteur Face ID sous l’écran
Partenaires : Actualité iPhone - Culture Geek
©2009-2025 i2CMedia | A propos |