Kawaidi Fassarar Hausa
iOS Universel / Musique
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu yanuwa Musulmai,
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
Allah Yayi dadin tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammadu (Sallallahu alaihi wasallam).
Yabo da Godiya su kara tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda da ni'ima taSa ayyuka kyawawa ke kammaluwa.
Wannan sabuwar manhajja ce kuma irinta ta farko a wannan dandali na Apple App Store domin kawo muku cikakken littafin Kawa'idi domin ya kasance makarantar gida a gareku yanuwa Musulmi. Wanna manhajja ta Qawa'idi tana aiki ba tare da data ba wato offline take aiki.
A cikinta zaku samu:
1. kawa-idi fassarar hausa pdf
2. Littafin Kawa'idi Audio wato kawa'idi mp3 mai dauke da sauti inda malam ke karantawa da fassarawa sannu a hankali tamkar dai kuna daukar karatun a gaban malami a makaranta.
3. FASSARAR LITTAFIN KAWA-IDI DA HAUSA
4. Kawaidi Warash wato kawa idi arabic mai dauke da rubutun larabcin wato dai Litttafin Kawa'idi Rubutun Hannu Na Warash
5. littafin kawa-idi fassarar hausa mai kaloli domin fahimtar ma'anonin daidaikun kalmomin littafin na kawa idi
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W). Bayan haka, Wannan littafi ne da yake bayani a kan Tauhidi a addinin Musulunci cikin harshen Hausa, domin amfanin Musulmi kasancewar wannan hanya mafi sauki wajen yada sako a cikin fadin duniya ga miliyoyin mutane, sabanin tsohuwar hanya ta buga littafi a rarraba shi, da fatan za’a samu wani wanda zai dauki nauyin wannan aiki a matsayin Sadakatul Jariya domin cigaba da gudanar da wannan aiki na alkhairi ta yadda wata rana zai zamto akwai tarin littattafai masu yawa cikin harshen Hausa kyauta domin yada addinin Allah. ƙawaidi hausa
Abubuwan dake cikin wannan littafin na qawa idi fassarar hausa :
1. Akidodin Tawhidi (الْعَقَائِدُ التَّوْحِيدِيَّةُ)
2. ƙa’idodin Sallah (قواعد الصلاة)
3. Babin Farillan Sallah (بَابُ فَرَائِضِ الَصَّلاَةِ)
4. Babin Sunnonin Sallah (بَابُ سُنَنِ الصَّلاَةِ)
5. Mustahabban Sallah (فَضَائِلِ الصَّلاَةِ)
6. Babin wankan da yake wajibi (بَابُ مُوجِبَاتِ الْغُسْلِ)
7. Babin cikin wanka na sunnah (بَابُ فِي الْغُسْلِ الْمَسْنُونِ)
8. Babin cikin Salloli na sunnah (بَابُ فِي الصَّلاَةِ الْمَسْنُونِ)
9. Babin ƙa’idojin Musulunci (بَابُ قَوَاعِدِ الْإِسْلاَمِ)
10. Babin Sujjada gabanin/kafin Sallama wato sujjada qabli (بَـابٌ فِي السُّجُودِ قَبْلَ السَّلاَمِ)
11. Babin Sujjada bayan Sallama wato sujjada ba'adi (بَابٌ فِى السُّجُودِ الْبَعْدِيِّ)
12. Babi acikin rafkanuwar da babu sujjada acikinsa (بَابٌ فِى السَّهْوِ اَلَّذِ لاَ سُجُودُ فِيهِ،)
13. Babin Farillan Alwala (بَابٌ فَرَائِضِ الْوُضُوءِ)
14. Babin Sunnonin Alwala (بَابٌ سُنَنِ الْوُضُوءِ)
15. Babin Mustahabban Alwala (بَابٌ فَضَائِلِ الْوُضُوءِ)
16. Babin Farillan taimama (بَابٌ فَرَائِضِ التَّيَمُّمِ)
17. Babin Sunnonin Taimama (بَابٌ سُنَنُ التَّيَمُّمِ)
18. Babin sunnonin Wanka (بَابٌ سُنَنُ الْغُسْلِ)
19. Babi acikin Mustahabban Wanka (بَابٌ فِي فَضَائِلِ الْغُسْلِ)
20. Ma’anar Kalmar Shahada wato kalmar Tauhidi - Laa iLaaha iLLallahu (معنى لا إله إلا الله)
21. Murshida - waɗannan Aqidojin Ahlus Sunna ne wadda ake kira da “Murshida” (الْمُرْشِدَةِ)
22. Fa'ida - Wata fa’ida acikin ambaton sashin abinda saninsa yakamata (فَائِدَةٌ فِي ذِكْرِبَعْضِ مَا يَنْبَغِي تَعَلُّمُهُ
)
23. Karanci maanar tahiya a Sallah - Tahiyar Sallah (اَلتَّشَهُّدُ فِي الصَّلَاةِ)
24. AlKunutu (القنوت)
25. Salatul Ibrahimiyya wanda Annabi ya koyar da sahabbai (الصلاة الإبراهيمية)
26. Sayyidul istigfari - Shugaban Istighfari (سيد الإستغفار)
27. Addu'ar Neman Zabi - addu'ar istikara (دُعَاءُ الْإِسْتِخَارَةِ)
Annabi (s.a.w) yace: Duk wanda ya yada aikin alkhairi, yana da lada kwatankwacin na wanda ya aikata wannan aikin alkhairi. Don haka ku aika da wannan manhajja zuwa ga yanuwa musulmai ta kafafenku na sadarwa domin ya zama sadaka mai gudana a gareku damu baki daya.
Domin tuntubata kareemtkb@gmail.com
Nagode.