Littafin Ahalari Da Hausa
iOS Universel / Musique
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh,
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) bayan haka,
Wannan manhajja ce domin kawo muku cikakken Littafin Ahalari mai dauke da rubutun larabci da kuma fassarar Hausa kana tana aiki ba tare da data ba. Ahalari Warash fassarar Hausa dominku. Fassarar Littafin Ahdhari
مختصر الأخضري في الفقه المالكي - الكتاب مترجم إلى لغة الهوسا
مختصر العلامة الأخضري في العبادات على مذهب الإمام مالك
Wannan manhajja ta mukhtasarul Akhdari ta ƙunshi muhimman bangarori guda uku:
1. Rubutaccen littafin Ahalari mai dauke da fassarar Hausa. A wannan sashe zaku samu littafin alAkhdari mai dauke da rubutun larabci kana da fassarar Hausa bi da bi. Domin sauƙin dubawa akwai mazaɓa inda zaku iya zuwa kan kowanne fasali cikin sauƙi. Domin samun jerin fasalolin dake ciki sai ku danna alama dake sama-maso-dama na shafin farko na wannan mahaja.
2. Bayan sashen rubutaccen ahalarin sai kuma sashen littafin ahalari bugon warsu. A wannan sashe akwai cikakken littafin akhdari daga bango zuwa bango mai dauke da ahalari warash salon rubutun allo irin namu na tsangaya. Kana an ƙawata wannan sashe da launuka wato kaloli domin sauƙin dubawa. Ga ma'anar launukan kamar haka:
2.1 Launin shuɗi na nuni da Fasali
2.2 Launin Ja na nuni da Farali wato abun da ya wajaba wanda idan babu shi aiki kan ɓaci.
2.3 Launin kore na nuni da sunna ko sunnoni
2.4 Launin rawaya wato ruwan ɗorawa na nuni da mustahabbi
2.5 Sai launin pink wanda ke nuni da bayani kan hukunce-hukuncen rafkanuwa
3. A sashe na uku kuma zaku samu littafin ahalari audio mp3 wato dai ahalari sauti inda malam ke karantawa da kuma fassara littafin na ahalari. Malam ya biyo karatun daki-daki kana yana yi yana maimaitawa domin dai karatun ya shigi kunnen mai sauraro. Allah ya sakawa malam da gidan Aljannah ameen. A wannan sashi na alakhdari audio zaku iya maimaita sauti sau ba adadi wato (REPEAT SINGLE TRACK) ko kuma ku maimaita duka wato (REPEAT ALL) ko ku rufe maimaicin baki daya. Domin waɗannan zaɓuka sai ku danna alamar maimaici wato REPEAT BUTTON dake ƙasa-maso-dama na shafin ahalari audio-player. Kana zaku iya zaɓar sauti a matsayin FAVOURITE.
Toh yanuwa musulmi, wannan manhajja ta ahalari itace irinta ta farlo a wannan dandali na Apple App Store don haka kada ku bari a baku labari. Sau da dama idan za'a yiwa mutum gorin karatu ko ilimin addini, akance "Wa, wannan da ko ƙawa'idi bai iya ba ballantana ahalari..." matuƙar ka sauke wannan manhajja ka kuma saurareta da karantata da kyau toh ahalari kam sai dai ka ɗorawa wani karatunsa in Allah Ya so. Yi maza ka/ki sauke ka/ki koyi ahalari kada abokai ko ƙawaye su rigaka/ki.
Daga bisani idan kunji daɗin wannan manhajja ta littafin ahlari toh ku aika ta zuwa ga yanuwa musulmi ta kafafenku na sadarwa. Allah Ya amsa daga garemu baki ɗaya Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum.
Domin samun waɗansu manhajjoji irin wannan kamarsu kawaidi fassarar Hausa, ishimawi, iziyya, risala, muwaɗɗa malik da dai sauransu, sai ku aiko mana da saƙo ta adireshinmu kareemtkb@gmail.com ku ambaci sunan manhajjar da kukeso a ƙirƙira muku. Manhajjar da tafi yawan mabuƙatanta ita zamu fi mai da hankali waken ƙirƙira in shaa Allahu.
تحميل كتاب متن الأخضري في العبادات على مذهب الإمام مالك
Da fatan zaku ji daɗin wannan mahaja ta ahalari fassarar hausa
littafin ahalari fassarar hausa pdf
fassarar littafin ahlari
littafin ahalari mai fassarar hausa
ahalari fassarar hausa complete
Zaku iya canja tsarin manhajjar tsakanin haske da duhu wato light/dark mode.
Tsira da Aminci suƙara tabbatuwa ga fiyayyen halitta Annabinmu Muhammadu (s.a.w). Wassalamu alaikum wa rahmatullah.